14. Al'umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”
15. Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”
16. Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta.
17. Allah da yake hasken Isra'ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.
18. Jeji mai dausayi da ƙasar noma za a lalatar da su ƙaƙaf, kamar yadda ciwon ajali yake hallaka mutum.