3. Ubangiji ya ce,“Sun tanƙwasa harshensu kamarbaka,Ƙarya ce take rinjayar gaskiya aƙasar.Suna ta cin gaba da aikata mugunta,Ba su kuwa san ni ba.
4. “Bari kowane mutum ya yi hankalida maƙwabcinsa,Kada kuma ya amince da kowaneirin ɗan'uwa,Gama kowane ɗan'uwa munafukine,Kowane maƙwabci kuma mai kushene.
5. Kowane mutum yana ruɗinmaƙwabcinsa da abokinsa,Ba mai faɗar gaskiya,Sun koya wa harshensu faɗarƙarya.Suna aikata laifi,Sun rafke, sun kasa tuba.
6. Suna ƙara zalunci a kan zalunci,Yaudara a kan yaudara,Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.
7. Saboda haka, Ubangiji MaiRunduna, ya faɗa cewa,“Zan tsabtace su, in gwada su,Gama me zan yi kuma sabodajama'ata?
8. Harshensu kibiya ce mai dafi, yanafaɗar ƙarya,Kowa yana maganar alheri damaƙwabcinsaAmma a zuciyarsa yana shirya masamaƙarƙashiya.