Irm 8:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa,Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!

19. Ku ji kukan jama'ata ko'ina aƙasar,“Ubangiji, ba shi a Sihiyonane?Sarkinta ba ya a cikinta ne?”Ubangiji ya ce,“Me ya sa suka tsokane ni dasassaƙaƙƙun gumakansu,Da baƙin gumakansu?”

20. Mutane suna ta cewa,“Damuna ta ƙare, kaka kuma tawuce,Amma ba a cece mu ba.”

Irm 8