Irm 52:30-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba'in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4.600).

31. A shekarar da Ewil-merodak ya zama Sarkin Babila, sai ya nuna wa Yekoniya Sarkin Yahuza alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yekoniya bauta.

32. Ewil-merodak ya nuna wa Yekoniya alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babila tare da shi.

33. Yekoniya ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa.

34. Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarki, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.

Irm 52