Irm 51:48-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

48. Sa'an nan sama da duniya, da dukanabin da take cikinsu,Za su raira waƙar farin ciki,Domin masu hallakarwa daga arewada za su auko mata,Ni Ubangiji na faɗa.”

49. Babila za ta fāɗi,Saboda mutanen Isra'ila da dukanmutanen duniya waɗanda takashe.

50. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!Ku gudu! Kada ku tsaya!Ku tuna da Ubangiji a can nesa indakuke,Ku kuma yi ta tunawa daUrushalima.

51. Mun sha kunya saboda zargin da akeyi mana,Kunya ta rufe mu,Gama baƙi sun shiga tsarkakanwurare na Haikalin Ubangiji.

52. “Domin haka kwanaki suna zuwa,”in ji Ubangiji,“Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila, da dukan ƙasarta,Waɗanda aka yi wa rauni, za su yinishi.

53. Ko da Babila za ta hau samaniya,Ta gina kagara mai ƙarfi a can,Duk da haka zan aiki masuhallakarwa a kanta,Ni Ubangiji na faɗa.”

54. Ku ji muryar kuka daga Babila,Da hargowar babbar hallakarwadaga ƙasar Kaldiyawa!

55. Gama Ubangiji yana lalatar daBabila,Yana kuma sa ta kame bakinta naalfarma,Sojoji suna kutsawa kamar raƙumanruwa,Suna ta da muryoyinsu.

56. Gama mai hallakarwa ya auka waBabila,An kama sojojinta,An kuma kakkarya bakunansu,Gama Ubangiji shi Allah ne, maisakayya,Zai yi sakayya sosai.

57. “Zan sa mahukuntanta, da masuhikimarta,Da masu mulkinta, dashugabanninta,Da sojojinta su sha su yi maye.Za su dinga yin barcin da ba za sufarka ba,”In ji Sarkin, mai suna Ubangiji MaiRunduna.

58. “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,Za a baje garun nan na Babila maifāɗiZa a kuma ƙone dogayenƙyamarenta da wuta.Mutane sun wahalar da kansu abanza.Sauran al'umma sun yi wahala kawaidomin wutar lalata.”

Irm 51