Irm 50:43-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Sarkin Babila ya ji labarinsu,Hannuwansa suka yi suwu.Wahala da azaba sun kama shikamar mace mai naƙuda.

44. “Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da yake fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa'an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni?

45. Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango.

46. Duniya za ta girgiza sa'ad da ta ji an ci Babila da yaƙi. Za a ji kukanta cikin sauran al'umma.”

Irm 50