Irm 50:2-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ku ba da labari ga sauranal'umma, ku yi shela,Ku ta da tuta, ku yi shela,Kada ku ɓuya, amma ku ce,‘An ci Babila da yaƙi,An kunyatar da Bel,An kunyatar da siffofinta,Merodak ya rushe,Gumakanta kuma sun ragargaje!’

3. “Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”

4. Ubangiji ya ce, “Sa'ad da lokacin nan ya yi, mutanen Isra'ila da na Yahuza za su zo tare, suna kuka, suna nemana, ni Ubangiji Allahnsu.

Irm 50