Irm 48:35-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Zan hana mutanen Mowab miƙa hadayu na ƙonawa a tuddai, da miƙa wa gumakansu sadaka, ni Ubangiji na faɗa.

36. “Zuciyata tana makoki domin Mowab da Kir-heres kamar wanda yake kukan makoki da sarewa saboda wadatarsu ta ƙare.

37. Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.

38. Ba abin da ake yi a bisa kan soraye da dandali na Mowab sai baƙin ciki, gama na farfashe Mowab kamar tulun da ba a so, ni Ubangiji na faɗa.

39. An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda suke kewaye da ita.

Irm 48