Irm 46:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma.

2. Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.

3. Masarawa suka yi ihu, suka ce,“Ku shirya kutufani da garkuwa,Ku matso zuwa wurin yaƙi!

4. Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, kuhau!Ku tsaya a wurarenku da kwalkwalia ka!Ku wasa māsunku!Ku sa kayan yaƙi!”

5. Ubangiji ya yi tambaya ya ce,“Me nake gani?Sun tsorata, suna ja da baya,An ci sojojinsu, suna gudu,Ba su waiwayen baya, akwai tsoro akowane sashi.”

6. Masu saurin gudu ba za su tsere ba,Haka nan kuma jarumi,A arewa a gefen Kogin Yufiretis,Sun yi tuntuɓe, sun fādi.

Irm 46