9. Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima?
10. Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.
11. “Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.
12. Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.
13. Zan hukunta dukan waɗanda suke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba.