Irm 43:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama'a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba.

5. Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al'ummai, inda aka kora su,

6. mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.

7. Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.

8. Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce,

9. “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza,

10. ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.

Irm 43