1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya bayan da Nebuzaradan shugaban matsara ya sake shi daga Rama, sa'ad da ya yi masa ƙuƙumi tare da waɗanda aka kwaso daga Urushalima da Yahuza, za su Babila.
2. Shugaban matsara ya ware Irmiya, sa'an nan ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ne ya hurta wannan masifa a kan wurin nan.
3. Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku.
4. Yau na kwance ƙuƙumin da yake a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”