9. Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”
10. Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama'an nan da Urushalima, da ka ce musu, ‘Za ku zauna lafiya,’ amma ga shi, takobi zai sassare su.”
11. Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama'ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba!