Irm 4:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,“Ku kafce saurukanku,Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.

4. Ya ku mutanen Yahuza da naUrushalima,Ku yi wa kanku kaciya dominUbangiji,Ku kawar da loɓar zukatankuDon kada fushina ya fito kamarwuta,Ya cinye, ba mai iya kashewa,Saboda mugayen ayyukan da kukaaikata.”

5. “Ku yi shela a cikin Yahuza,Ku ta da murya a Urushalima, kuce,‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,‘Ku tattaru, mu shiga birane masugaru.’

6. Ku ta da tuta wajen Sihiyona!Ku sheƙa a guje neman mafaka,kada ku tsaya!Gama zan kawo masifa da babbarhalaka daga arewa.

7. Zaki ya hauro daga cikinruƙuƙinsa,Mai hallaka al'ummai ya kamahanya,Ya fito daga wurin zamansa don yamai da ƙasarku kufai,Ya lalatar da biranenku, su zamakango, ba kowa.

8. Domin haka sai ku sa tufafinmakoki,Ku yi makoki ku yi kuka,Gama fushin Ubangiji bai rabu damu ba.”

9. Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”

Irm 4