Irm 31:30-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Amma kowa zai mutu sabodazunubin kansa,Wanda ya ci inabi masu tsami,Shi ne haƙoransa za su mutu.”

31. Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.

32. Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.

33. Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.

34. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

35. Haka Ubangiji ya ce,Shi wanda ya ba da rana ta haskakayini,Ya sa wata da taurari su ba da haskeda dare,Shi ne yakan dama teku, ya saraƙumanta su yi ruri,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

Irm 31