Irm 31:19-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3-4. Ubangiji ya bayyana gare ni tundaga nesa cewa,“Ya Isra'ila, budurwa!Na kusace ki da madawwamiyarƙaunata,Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata agare ki ba.Zan sāke gina ki,Za ki kuwa ginu,Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe,Za ki shiga rawar masu murna.

19. Gama na tuba saboda na rabu dakai,Bayan da aka ganar da ni, sai nasunkuyar da kai,Kunya ta kama ni, na gigice,Domin ina ɗauke da wulakancinƙuruciyata.’

20. Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccenɗana ba ne?Ashe, shi ba ɗan gaban goshina bane?A duk lokacin da na ambace shi akan muguntarsaNakan tuna da shi da ƙauna.Saboda na ƙwallafa zuciyata akansa,Hakika zan yi masa jinƙai, niUbangiji na faɗa.”

21. Ki kafa wa kanki alamun hanya,Ki kafa wa kanki shaidu,Ki lura da gwadabe da kyau,Hanyar da kin bi, kin tafi.Ya budurwa Isra'ila, ki komo,Komo zuwa biranen nan naki.

22. Har yaushe za ki yi ta shakka,Ya ke 'yar marar bangaskiya?Gama Ubangiji ya halitta sabon abua duniya,Mace ce za ta kāre namiji.”

23. Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu.‘Ubangiji ya sa maka albarka,Ya wurin zaman adalci,Ya tsattsarkan tudu!’

24. Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu.

25. Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

26. Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”

27. “Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza.

28. Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.

29. A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa,‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masutsami,Haƙoran 'ya'ya suka mutu’ ba.

30. Amma kowa zai mutu sabodazunubin kansa,Wanda ya ci inabi masu tsami,Shi ne haƙoransa za su mutu.”

31. Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.

32. Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.

Irm 31