8. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “A wannan rana zan karya karkiya da take a wuyansu, in cire musu ƙangi, ba kuma za su ƙara zama bayin baƙi ba.
9. Amma za su bauta mini, ni Ubangiji Allahnsu, da Dawuda sarkinsu, wanda zan tayar musu da shi.”
10. Ubangiji ya ce,“Kada ka ji tsoro, ya baranaYakubu,Kada kuma ka yi fargaba, yaIsra'ila,Gama zan cece ka daga ƙasa mainisa,Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasarbautarsu.Yakubu zai komo, ya yi zamansa raia kwance,Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.
11. Gama ina tare da kai don in cece ka,Zan hallaka dukan al'ummai sarai,Inda na warwatsa ku.Amma ku ba zan hallaka ku ba,Zan hore ku da adalci,Ba yadda za a yi in ƙyale ku bahukunci,Ni Ubangiji na faɗa.”
12. Ubangiji ya ce,“Rauninku ba ya warkuwa,Mikinku kuwa mai tsanani neƙwarai.
13. Ba wanda zai kula da maganarku,Ba magani domin mikinku,Ba za ku warke ba.