1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,
2. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, ‘Ka rubuta dukan maganar da na faɗa maka a littafi.
3. Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.”
4. Waɗannan ne maganar da Ubangiji ya faɗa a kan Isra'ila da Yahuza.