Irm 29:20-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.’

21. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. ‘Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.

22. Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la'ana cewa, “Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!”

23. Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.

24. “Zancen Shemaiya mutumin Nehelam,

Irm 29