Irm 28:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila.

4. Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”

5. Sa'an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama'ar da suke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce,

6. “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila.

7. Amma yanzu sai ka ji maganan nan da zan faɗa maka, kai da dukan jama'an nan.

8. Annabawan da suka riga mu, ni da kai a zamanin dā, sun yi wa ƙasashe masu yawa da manyan mulkoki annabcin yaƙi da yunwa, da annoba.

9. Idan maganar wannan annabi kuwa da ya yi annabcin salama ta cika, sa'an nan ne za a sani gaskiya Ubangiji ne ya aiko shi.”

10. Sai annabi Hananiya ya cire karkiyar daga wuyan annabi Irmiya ya karya ta.

11. Sa'an nan Hananiya ya yi magana a gaban dukan jama'a, ya ce, “In ji Ubangiji, haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, daga wuyan dukan al'ummai kafin shekara biyu.” Sai annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.

Irm 28