1. Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce,
2. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Na karya karkiyar Sarkin Babila.
3. Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila.