Irm 23:33-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. “Kai Irmiya, sa'ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, ‘Mece ce nawayar Ubangiji?’ Sai ka ce masa, ‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,’ ni Ubangiji na faɗa.

34. Idan annabi ko firist, ko wani daga cikin jama'a, ya ce, ‘Nawayar Ubangiji,’ zan hukunta shi duk da iyalin gidansa.

35. Haka kowannenku zai ce wa maƙwabcinsa da ɗan'uwansa, ‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?’

36. Amma ba za ku ƙara ambatar nawayar Ubangiji ba, gama maganar kowane mutum za ta zama nawaya, ga shi, kun ɓata maganar Allah mai rai, Ubangiji Mai Runduna, Allahnmu.

37. Haka za ka faɗa wa annabi, ‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?’

38. Amma idan kun ce, ‘Nawayar Ubangiji,’ ga abin da ni Ubangiji na ce, tun da yake kun faɗi wannan magana, wato ‘Nawayar Ubangiji,’ alhali kuwa na aika muku cewa, kada ku ce, ‘Nawayar Ubangiji,’

39. saboda haka, hakika zan ɗaga in jefar da ku daga gabana, da ku da birni wanda na ba ku, ku da kakanninku.

40. Zan sa ku zama abin zargi da abin kunya har abada, ba kuwa za a manta da wannan ba.”

Irm 23