Irm 23:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Suna ta faɗa wa waɗanda suke rainamaganar Ubangiji cewa,‘Za ku zauna lafiya!’Ga kowane mai bin nufin tattaurarzuciyarsa,‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”

18. Irmiya ya ce, “Gama wane ne a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wane ne ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa?

19. Ga shi, hadirin hasalar Ubangiji yataso,Kamar iskar guguwa,Zai tashi a bisa kan mugaye.

20. Ubangiji ba zai huce ba,Sai ya aikata nufin zuciyarsa.Amma sai daga baya za ku ganesarai.”

21. Ubangiji ya ce,“Ni ban aiki waɗannan annabawaba,Duk da haka sun tafi,Ban kuwa yi musu magana ba,Amma sun yi annabci.

22. Amma da a ce sun tsaya cikinshawarata,Da sun yi shelar maganata gajama'ata,Da sun juyar da su daga muguwarhanyarsu,Da mugayen ayyukansu.

23. “Ni Allah na kusa ne kaɗai,Banda na nesa?” In ji Ubangiji.

24. “Mutum ya iya ɓoye kansa a wanilunguInda ba zan iya ganinsa ba?” In jiUbangiji.“Ashe, ban cika sammai da duniyaba?

25. Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’

26. Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?

27. Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al.

Irm 23