Irm 22:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ya biya wa matalauta da masubukata hakkinsu,Ya kuwa yi kyau.Abin da ake nufi da sanina ke nan,In ji Ubangiji.

17. Amma ka sa idonka da zuciyarka gaƙazamar riba,Da zubar da jinin marar laifi,Da yin zalunci da danniya.

18. Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza,“Ba za su yi makoki dominsa ba, kosu ce,‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo'yar'uwarmu!’Ba za su yi makoki dominsa ba, suce,‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’

19. Za a binne shi kamar jaki,Za a ja shi a yar a bayan ƙofofinUrushalima.”

20. Ku haura zuwa Lebanon, ku yikuka,Ku ta da muryarku cikin Bashan,Ku yi kuka daga Abarim,Gama an hallakar da dukanƙaunatattunku.

21. Ubangiji ya yi muku magana alokacin wadatarku.Amma kun ce, “Ba za mu kasakunne ba!”Wannan shi ne halinku tun kunasamari,Don ba ku yi biyayya da muryaUbangiji ba.

Irm 22