10. Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”
11. “Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji,
12. Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce,Ku aikata adalci kowace safiya.Ku ceci wanda aka yi masa ƙwacedaga hannun mai matsa masa,Don kada hasalata ta tashi kamarwuta,Ta yi ƙuna, har ba mai iya kasheta,Saboda mugayen ayyukanku.