Irm 2:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Domin haka, ni Ubangiji zangabatar da ku gaban shari'a,Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan'ya'yanku, wato jikokinku.

10. Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajenyamma, ku gani,Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, kuduba da kyau,A dā an taɓa yin wani abu haka?

11. Akwai wata al'umma da ta taɓasāke gumakantaKo da yake su ba kome ba ne?Amma mutanena sun sauya darajarsuda abin da ba shi da rai.

12. Sammai, ku girgiza saboda wannan,ku razana,Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.

Irm 2