8. Zan mai da wannan birni abin ƙyama, abin raini, dukan wanda ya wuce wurin zai yi mamaki, ya yi tsaki saboda dukan masifun da suka auka wa birnin.
9. Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’
10. “Sa'an nan sai ka fasa tulun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai,