Irm 17:19-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima.

20. Ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.

21. Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima.

22. Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.’

Irm 17