1. Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu.
2. Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi.
3. Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.