Irm 16:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ba za ka yi aure ka haifi 'ya'ya mata da maza a wannan wuri ba.

3. Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan 'ya'ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa,

4. za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”

Irm 16