Irm 14:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Saboda ƙasar ta bushe,Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,Manoma sun sha kunya,Suka lulluɓe kansu don kunya.

5. Barewa ma a saura takan gudu,Ta bar ɗanta sabon haihuwa,Domin ba ciyawa.

6. Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddanda ba ciyawa,Suna haki kamar diloli,Idanunsu ba su ganiDomin ba abinci.”

7. Irmiya ya ce,“Ko da yake zunubanmu su neshaidunmu,Ya Ubangiji, ka yi taimako sabodasunanka!Gama kāsawarmu ta yi yawa,Domin mun yi maka zunubi.

8. Ya kai, wanda kake begen Isra'ila,Mai Cetonta a lokacin wahala,Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar?Kamar matafiyi wanda ya kafaalfarwarsa a gefen hanya don yakwana, ya wuce?

9. Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai sanabin da zai yi ba,Kamar jarumin da ya kasa yinceto?Duk da haka, ya Ubangiji, kana nana tsakiyarmu.Da sunanka ake kiranmu,Kada ka bar mu!”

10. Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”

11. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan.

Irm 14