Irm 12:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ubangiji ya ce,“Na bar jama'ata.Na rabu da gādona,Na ba da wanda raina yake ƙauna ahannun maƙiyansa.

8. Abin gādona ya zama mini kamarzaki a cikin kurmi,Ya ta da murya gāba da ni,Domin haka na ƙi shi.

9. Ashe, abin gadon nan nawa ya zamadabbare-dabbaren tsuntsun nan nemai cin nama?Tsuntsaye masu cin nama sun kewayeshi?Tafi, ka tattaro namomin jeji,Ka kawo su su ci.

10. Makiyaya da yawa sun lalatar dagonar inabina.Sun tattake nawa rabo,Sun mai da nawa kyakkyawan rabokufai da hamada.

11. Sun maishe shi kufai, ba kowa,Yana makoki a gare ni,Ƙasar duka an maishe ta kufai,Amma ba wanda zuciyarsa ta damu akan wannan.

Irm 12