15. Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.
16. Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.
17. Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”