Irm 1:17-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.

18. Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.

19. Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”

Irm 1