1. Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus.
2. Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.
3. Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne.
4. Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.
5. Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.