1. Daga Bulus, manzo, ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta wurin wani mutum ba, sai dai ta wurin Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu,
2. da kuma dukan 'yan'uwa da suke tare da ni, zuwa ga ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.
3. Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu,
4. wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin yă cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu.