19. 'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.
20. Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.
21. 'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.
22. 'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri.
23. Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.
24. 'Ya'ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora.