Fit 39:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

3. An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.

4. Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.

5. Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Fit 39