Fit 37:21-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin.

22. An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe.

23. Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.

Fit 37