1. Sai Musa ya tattara dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi.
2. Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.
3. Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”