Fit 34:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.

2. Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina'i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen.

Fit 34