15. Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.
16. Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.
17. Ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’
18. Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’