Fit 29:31-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Sai ka ɗauki naman ragon keɓewa, ka dafa shi a wuri mai tsarki.

32. Haruna da 'ya'yansa maza za su ci naman da abinci da yake a cikin kwandon a ƙofar alfarwa ta sujada.

33. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.

Fit 29