28. Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran.
29. Duk sa'ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai ɗauki sunayen 'ya'yan Isra'ila a gaban Ubangiji kullum, a kan ƙyallen maƙalawa domin nemar musu nufin Allah.
30. Za ku kuma sa Urim da Tummin a kan ƙyallen maƙalawar domin su kasance a zuciyar Haruna sa'ad da ya shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai kokekoken Isra'ilawa a gaban Ubangiji.
31. “Sai ku yi taguwar falmaran da shuɗi duka.
32. Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa'an nan a yi wa wuyan basitsa, wato cin wuya, domin kada ya kece.