1. “Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba'i.
2. A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.
3. Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.