7. da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
8. Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su.
9. Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”
10. “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.
11. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya.