12. Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra'ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
13. Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama'ar shari'a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.
14. Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”
15. Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.