Fit 18:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yetro, firist na Madayana, surukin Musa, ya ji dukan abin da Allah ya yi wa jama'arsa, wato Musa da Isra'ilawa, yadda Ubangiji ya fito da su daga Masar.

2. Ya kawo Ziffora matar Musa, wadda Musa ya aika da ita gida.

Fit 18