20. Sai suka ci gaba da tafiya daga Sukkot suka yi zango a Etam a gefen jejin.
21. Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al'amudin girgije, da dare kuwa da al'amudin wuta, domin ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana.
22. Al'amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama'a jagora ba.