27. Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.”’ Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.
28. Isra'ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
29. Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi.
30. Da dare Fir'auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.